Ba zan iya jagorancin Lebanon ba-Hariri
Firaministan Labanon Saad Hariri da aka zaba domin kafa sabuwar sabuwar gwamnati ya yi watsi da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda, yana mai cewa, ba zai iya jagoranci ba a daidai wannan lokaci da kasar ke cikin gagarumar matsalar tattalin ariziki mafi muni a tarihita.
Wallafawa ranar:
A watan Octoban 2020 ne aka zabi Hariri a matsayin Firaministan da zai kafa gwamnatin da aikinta shi ne sake fasalta hanyoyin samar da tattalin arizikin kasar da zai kai ga kasar ta cimma tallafin farfado da tattalin arizikin na kasshen duniya.
Hariri ya sanar da 'yan jarida cewa ya gana da shugaban kasar Michel Aoun da ya bukaci ya sake fasalta shawarar jerin sunayen ministocin da za su shiga sabuwar gwamnatin da ya gabatar, wanda a kansa shi kuma ya nuna turjiya.
Da yake tsokaci kan janyewar da ke zuwa 'yan kwanaki kafin zagayowar ranar faruwar mummunan hadarin tashar jiragen ruwan Beirut, Ministan Harakokin Wajen Faransa Yves Le Drian ya danganta lamarin da ya faru a matsayin kullallen makirci dai ya buda sabon babi a fagen siyasar kasar sai dai ya ce har yanzu akwai sauran lokacin yin gyara.
Wannan lamari in ji shi zai sa tarihi ya waiwayi shuwagabanin siyasar kasar ta Labanon nan gaba domin amsa kuskuren da suka aikata
Ita ma da kanta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bakin cikinta kan matakin da Haririn ya dauka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu