Isa ga babban shafi
Lebanon - IRAN

Iran ta shirya sayar wa Lebanon Man Fetur duk da takunkumin Amurka

Iran ta ce a shirye ta ke ta ci gaba da saidawa gwamnatin Lebanon Mai don taimakata rage karancinsa da take fuskanta, kwanaki bayan isar man fetur din Iran na farko da kungiyar Hizbullah ta tsara  shiga kasar.

Motar dakon Mai dake shigowa zuwa Lebanon daga makwabta.
Motar dakon Mai dake shigowa zuwa Lebanon daga makwabta. AP - Bilal Hussein
Talla

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya ce "Idan gwamnatin Labanon tana son siyan man fetur daga gare su don magance matsalolin da yawan jama'arta ke fuskanta, za su samar mata"

Yayin jawabi ga wani taron manema labarai, jami’in yace tuni Iran ta saidawa wani dan kasuwar Lebanon din man fetur ba tare da ambatar Hizbullah ba.

Gidajen Mai a kasar Lebanon sun fara samun Man fetur daga Iran karkashin 'yan kasuwar Hezbollah.
Gidajen Mai a kasar Lebanon sun fara samun Man fetur daga Iran karkashin 'yan kasuwar Hezbollah. REUTERS - AZIZ TAHER

Hezbollah da ke samun goyon bayan Tehran ta yi alƙawari a watan Agusta cewa zata wadata kasar da  man fetur da zata rika daukowa daga Iran, domin rage radadin ƙarancin sa da ke haifar da hargitsi a Labanon, matakin da zai sabawa takunkumin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.