Isa ga babban shafi
Lebanon

Fira Ministan Lebanon ya ajiye aiki saboda fuskantar barazana

Fira ministan kasar Lebanon Sa’ad Hariri, ya sanar da sauka daga mukaminsa, bisa dalilan da ya ce sun hada da yunkurin da Iran ke yi na mamaye ikon tafiyar da gwamnatin kasar, sai kuma rayuwarsa da ke fuskantar barazana.

Fira Ministan kasar Lebanon Saad al-Hariri da ya ajiye aikinsa bisa fuskantar barazana ga rayuwarsa.
Fira Ministan kasar Lebanon Saad al-Hariri da ya ajiye aikinsa bisa fuskantar barazana ga rayuwarsa. REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

A cikin Nuwamban bara Sa’ad Hariri ya sake darewa kujerar Fira minitan Lebanon, bayan rike mukamin da yayi a tsakanin shekarun 2009 zuwa 2011.

A lokacin da yake gabatar da jawabin ajiye mukamin nasa, daga birnin Riyadh na Saudiyya Sa’ad Hariri ya zargi gwamnatin Iran da kungiyar mayakan Hezbollah da hadin baki wajen haddasa rikici a wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya, a kokarin mamaye harkokin kasashen.

Sai dai jim kadan da sanarwar ta Sa'ad Hariri kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Ghassemi ya musanta zargin da Fira ministan ya yi, tare da cewa, Sa'ad Hariri ya dauki matakin ne kawai, domin haddasa fitina a kasar ta Lebanon da sauran kasashen da ke yankin gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.