Lebanon
Hezbollah ta ce ba ta tsora hari daga Amurka ko Saudiyya
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ko gezau ba ta yi ba dangane da barazanar Amurka da Saudiyya na kai ma ta hari da kuma kakaba ma ta takunkumai, kwanaki bayan shugaba Donald Trump ya soke ta tare da kasar Iran.
Wallafawa ranar:
Talla
Shuagban kungiyar Hassan Nasrallah ya ce Hezbollah ba ta tsoron yaki da takunkumi ko kuma farfagandar kafofin yada labarai.
Nasrallah ya ce barazanar kisa ba ta dauke musu hankali, kamar dai yadda ya bayyana a sakon da ya aikewa magoya bayan sa dangane da cika shekaru 17 da janyewar Isra’ila daga kudancin Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu