Amurka za ta kafa takunkumi akan bankuna masu tallafawa Hezbollah
Majalisar wakilan kasar Amurka ta kada kuri’ar amincewa da wata doka da zai bata damar kafawa bankunan kasar takunkumi muddun aka samu ta na tallafawa kungiyar Hezbollah da kudi
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan Majalisun kasar baki daya ne suka amince da sabuwar dokar na yau laraba, dokar da zai bayar da damar kafa takunkumi akan duk bankin kasar dake da wata hada-hadar kuddade da kungiyar mazhabar Shia’a ta Hezbollah dake a kasar Labanan
Ana dai danganta kungiyar Hezbollah da gudanar da ayyuka sak irin na kungiyoyin ta’adda, hakazalika dokar na zuwa ne a yayin da kasar ta Amurka ke kokarin ganin ta dakile ayyukan kungiyar ISIL mai da’awar jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu