Isa ga babban shafi
Lebanon

An kashe kwamandan Hezbollah a Syria

Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta sanar da kisan babban kwamandanta da aka kashe a wani harin da aka kai a Syria kan sansanin mayakan da ke taimakawa dakarun Bashar al Assad yaki da ‘Ya tawaye.

Mustafa Badreddine Kwamandan Kungiyar Hezbollah
Mustafa Badreddine Kwamandan Kungiyar Hezbollah AFP
Talla

A yau Juma’a ne Hezobollah ta sanar da labarin kisan Mustafa Badreddine wanda ke jagorantar mayakan kungiyar domin taimakawa dakarun gwamnatin Syria yaki da ‘Yan tawaye.

An kashe shi ne a wani harin bom da aka kai kusa tashar jirgin sama a Damascus.

Sai dai zuwa yanzu Hezbollah ba ta ambaci wanda ta ke zargi ya kashe kwamadan ba sabanin yadda ta zargi Isra’ila a 2008 lokacin da aka kashe kwamandanta Imad da Badreddin ya gada.

Kungiyar tace yanzu tana gudanar da bincike

Badreddine dai na cikin jerin sunayen mutanen da Amurka da Isra’ila ke nama ruwa a jallo wanda ake zargi ya jagoranci kisan tsohon Firimiyan Lebanon Rafiq Hariri a 2005.

A yau Juma’a ne aka yi Jana’izar shi da asuba a kudancin Beirut, kuma yanzu babu wanda ya fito ya yi ikirarin daukar alhakin kisan shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.