Isa ga babban shafi

Sojojin Isra'ila sun kama mutane fiye da 20 da ake zargi da hannu a harin ranar 7 ga watan Oktoba

Rundunar sojin Isra’ila a yau Juma’a ta sanar da kama “fiye da ‘yan ta’adda 20 da ake kyautata zaton suna da hannu a  hare-haren Hamas a Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Asibitin Khan yunus a Gaza
Asibitin Khan yunus a Gaza via REUTERS - @MOHAMMEDHARAR2 VIA INSTAGRAM
Talla

Dakarun na Isra’ila da suka kutsa kai a cikin asibitin Nasser da ke Khan Younes a zirin Gaza,kasa da sa'o'i biyu kafin hakan, ma'aikatar lafiya ta Hamas ta sanar da cewa majinyata hudu da ke asibitin sun mutu sakamakon katsewar wutar lantarki da ta hana rarraba iskar oxygen bayan kwace asibitocin.

Harin Isra'ila a kudancin Lebanon
Harin Isra'ila a kudancin Lebanon AP - Ariel Schalit

"Sojojin Isra'ila sun gano makamai a cikin asibitin kuma sun kama mutane da dama da ake zargi da ta'addanci, ciki har da 'yan ta'adda fiye da 20 da suka shiga cikin kisan kiyashi na 7 ga Oktoba" a Isra'ila.

Dakarun Isra’ila sun kara da cewa suna ci gaba da gudanar  da buincike bayan gano cewa mayakan Hams sun yi amfani da wannan wuri a makonnin da suka gabata wajen kaiwa sojojin Isra'ila hari.

Palestinians displaced by the Israel air and ground offensive on the Gaza Striptake shelter near the border fence with Egypt in Rafah, Wednesday, Jan. 24, 2024.
Sansanin yan gudun hijira a Yankin Rafah AP - Hatem Ali

Rundunar ta Isara’ila ta sanar a jiya alhamis cewa ta kaddamar da wannan aiki kan wannan asibiti, wanda shi ne mafi girma a kudancin zirin Gaza, bayan samun “sahihan bayanai” da ke nuni da cewa Hamas ta yi garkuwa da wasu yan kasar Isra’ila.

Bayan shafe fiye da watanni hudu ana yaki tsakanin Isra'ila da Hamas, tashin hankalin ya fi karkata ne a kudancin zirin Gaza da aka yi wa kawanya, tsakanin garuruwan Khan Younes da Rafah, gari na karshe a kudancin yankin.

Yankin Zirin Gaza
Yankin Zirin Gaza REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA

Asibitin Nasser ya karbi dubban fararen hula da suka tsere daga yakin, wadanda wasunsu suka yi gudun hijira a cikin 'yan kwanakin nan cikin rudani, yayin da fadan da ake gwabzawa tsakanin sojoji da kungiyar Hamas ke kara kusantowa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.