Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen duniya 50 ne za su halarci taron tsaro na Munich a shekarar nan

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bude taron tsaro na Munich na 60 a Juma’ar nan, inda ake sa ran halartar shugabannin kasashe 50 a wannan shekarar.

Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris yayin jawabinta a taron Munich na wannan shekafrar.
Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris yayin jawabinta a taron Munich na wannan shekafrar. © AP - KAI PFAFFENBACH
Talla

Manyan maudu’an da za a tattauna a taron tsaron na wannan shekarar dai sun hada da yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Ukraine da Rasha, da kuma wanda ke gudana tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta gabatar da jawabi a wannan rana ta bude taron da za a shafe kwanaki uku ana yi.

A ranar Asabar kuwa, shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky za su gabatar da nasu jawabin.

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog da ministan harkokin wajen kasar, Israel Katz za su halarci taron, tare da wasu manyan wakilai daga mahukuntan Falasdinawa, sai wakilan gwamnatocin Saudiyya, Qatar, Masar da Jordan.

Wani mahimmin batu da ake sa ran tattaunawa a gefen wannan taro kuwa shine, sakamakon zaben Amurka na 5 ga watan Nuwamba, da kuma abin da ka iya biyo baya idan tsohon shugaban kasar Donald Trump ya lashe zaben.

Tawagar majalisar dokokin Amurka mai wakilai 30 da suka hada da ‘yayan jam’iyyar Trump na Republican za su halarci wannan taro.

Sai dai ba a gayyaci jami’an Rasha da na Iran ba taron tsaro na Munich na wannan shekarar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.