Isa ga babban shafi

Kusan mutane miliya 8 ne yakin Sudan ya tilasta wa tserewa daga muhallansu - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da yakin da ake a Sudan ya raba da muhallansu a halin yanzu ya kai miliyan 8. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 1 da dari 5 ne ke tsallakawa Sudan ta  Kudu kowace rana saboda yakin da ake yui.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 1 da dari 5 ne ke tsallakawa Sudan ta Kudu kowace rana saboda yakin da ake yui. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Filippo Grandi wanda ya ziyarci kasar Habasha, inda da dama daga cikin ‘yan gudun hijirar  suka nemi mafaka, ya bukaci kasashen da ke bada tallafi da su yi abin da suka saba wajen taimaka wa wadanda yaki ya daidaita, yana mai bayyana yanayin da suke ciki a matsayin mai tsanani. 

A watan Afrilun shekarar da ta gabata ne rikici ya barke a tsakanin rundunar sojin kasar, karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun kai daukin gaggawa na RSF, wanda mataimakinsa Janar Hamdan Daglo ke jagoranta. 

Tun daga wanna lokaci, sama da mutane dubu 100 ne suka tsallaka zuwa kasar Habasha daga Sudan, cikin su har da akwai ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka dubu 47.

Grandi ya kira da a taimaka cikin gaggawa don biyan bukatun wadannan ‘yan gudun hijira.

Karin wasu kasashe biyar da ke makwaftaka da Sudan ne suka karbi dimbim ‘yan gudun hijira daga Sudan. Sama da mutane rabin miliyan ne suka tsere zuwa Chadi tun daga watan Afrilu.

An yi kiyasin cewa mutane akalla dubu 1 da rai 5 ne ke arcewa zuwa Sudan ta Kudu a kowace  rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.