Sudan na bukatar dala Miliyan 150 saboda 'yan gudun hijirar Habasha - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan na bukatar akalla dala miliyan 150 domin taimakawa yan gudun hijirar da suka fito daga Habasha sakamakon tashin hankalin dake gudana a Yankin Tigray.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar kula da Yan gudun hijira na Majalisar Filippo Grandi ya bayyana haka bayan ya ziyarci inda aka tsugunar da Yan gudun hijira akalla 43,000 da suka samu mafaka a cikin kasar.
Grandi ya bukaci kungiyoyi da gwamnatocin dake bada agaji da su taimakawa Sudan wajen kula da wadannan baki domin ceto rayuwar su.
Rahotanni sun ce akalla Yan gudun hijira 500 zuwa 600 ke tsallakawa zuwa cikin Sudan kowacce shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu