WFP na shirin katse tallafin abinci ga ‘yan gudun hijira sama da miliyan 1 a Chadi
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ce a watan Janairu za ta kawo karshen tallafin abinci ga kimanin ‘yan gudun hijara miliyan 1.4 a kasar Chadi da suka hada da sabbin zuwa da suka tsere daga tashin hankali a yankin Darfur na kasar Sudan saboda karancin kudi.
Wallafawa ranar:
WFP ta kara da cewa matsalar kudi da karuwar bukatun jin kai sun tilastawa hukumar dakatar da bayar da agaji ga ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka a cikin gida daga Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kamaru daga watan Disamba.
Hukumar ta ce daga watan Janairu, dakatarwar zai shafi a ‘yan gudun hijira da ke cikin mawuyacin hali a Chadi, in ji WFP a ranar Talata a cikin wata sanarwa.
Fiye da 'yan gudun hijira 540,000 ne suka tsallaka daga Sudan zuwa kasar Chadi tun bayan yakin da ya barke watanni 7 da suka gabata tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF a cewar kungiyar kula da 'yan cirani ta duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu