Isa ga babban shafi

Arsenal ta murkushe West Ham da ci 6-0 a gasar Firimiya

Duniya – Kungiyar Arsenal ta lallasa West Ham United da ci 6-0 a gasar Firimiya ta Ingila, nasarar da ta sa kungiyar ta samu maki 52 a matsayi na 3, dai dai da makin Manchester City wadda ke matsayi na 2 bayan nasarar da ta samu na ci 2-1 a karawar da tayi da Everton.

Martin Odegaard da Bukayo Saka
Martin Odegaard da Bukayo Saka © AFP - ADRIAN DENNIS
Talla

Wannan nasarar ta dada tabbatar da yunkurin Arsenal na ci gaba da fafatawa wajen neman lashe gasar firimiyar a wannan shekara.

William Saliba ya jefawa Arsenal kwallon ta na farko a minti 32, yayin da Bukayo Saka ya ci ta 2 daga fenariti a minti 41.

A minti 44 Gabriel ya jefa ta 3, yayin da Leandro Trossard ya jefa ta 4 a minti 47, abinda ya nuna cewar a cikin mintina 13 Arsenal ta jefa kwallayen ta guda 4.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Saka ya jefa kwallo ta 5 a minti 63, sannan Declan Rice, tsohon kaftin din West Ham ya zirara ta 6 wadda kuma itace ta karshe.

Wannan itace rashin nasara mafi muni a tarihin West Ham tun bayan cin da Blackburn Rovers ta mata na 8-2 a shekarar 1963.

A karawar da aka yi jiya, Fulham ta doke Bournemouth da ci 3-1, kamar yadda Liverpool ta doke Burnley, sai kuma Tottenham ta samu nasara a kan Brighton da ci 2-1.

Newcastle ta samu galaba a karawar da suka yi da Nottingham da ci 3-2, sannan Bradford ta doke Wolverhampton da ci 2-0.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.