Isa ga babban shafi
GASAR AFCON

Afirka ta Kudu ta lashe tagullar AFCON 24

Afirka – Kasar Afirka ta Kudu ta samu nasarar lashe tagullar gasar AFCON dake gudana a Cote d'Ivoire, sakamakon nasarar da ta samu na doke Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da ci 6-5 a bugun fenariti.

Lokacin da 'yan wasan Afirka ta kudu suka ci fenariti na karshe a karawar su da DR Congo
Lokacin da 'yan wasan Afirka ta kudu suka ci fenariti na karshe a karawar su da DR Congo © Pierre René-Worms/RFI
Talla

An dai buga mintina 90 ba tare da kowacce kasa ta samu nasara ba, abinda ya kai ga zuwa bugun fenariti domin samun wanda zai samu matsayi na 3 a gasar baki daya.

Yayin bugun fenaritin Afirka ta Kudu ta jefa kwallaye 6, yayin da Congo ta jefa guda 5, bayan barar da damar da ta samu na cinye gasar.

Mai horar da 'yan wasan Afirka ta Kudu Hugo Broos
Mai horar da 'yan wasan Afirka ta Kudu Hugo Broos © Pierre René-Worms/RFI

Afirka ta Kudu ta fara zubar da budun fenaritin ta, yayin da ta jefa guda 4, sai kuma ita Congo ta jefa guda 4, amma ta barar da bugun ta na 5.

Bayan haka ne a ci gaba da bugu, inda Afirka ta kudu ta jefa guda 2, yayin da Congo ta ci guda, kuma golan Afirka ta Kudu Ronwem Williams ya tare guda.

Mai horar da 'yan wasan Afirka ta Kudu, Hugo Boss ya sake jaddada goyan bayan sa ga tawagar matasan kasar wanda ya bayyana cewar suna da makoma mai kyau a wasannin Afirka masu zuwa.

Masu sharhi a kan kwallon kafa sun yabawa tawagar 'yan wasan Afirka ta Kudu wadanda akasarin su sun fito ne daga wasan gida, sabananin akasarin kungiyoyin da suka shiga gasar ta AFCON.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.