Isa ga babban shafi
GASAR AFCON

Yau ake kammala gasar AFCON 24 da karawa tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire

cote d'ivoire – Yau ake saran kammala gasar cin kofin Afirka da ake yiwa lakabi da AFCON 2024 da wasan karshe tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire, kuma tuni birnin Abidjan ya yi cikar kwari da baki daga sassan Afirka da wasu kasashen duniya domin ganin yadda wasan zai kaya.

Victor Osimhen na Najeriya da Ousmane Diomandé a karawar da suka yi zagayen farko
Victor Osimhen na Najeriya da Ousmane Diomandé a karawar da suka yi zagayen farko AFP - FRANCK FIFE
Talla

Wadannan kasashe biyu na daga cikin wadanda suka yi fice wajen harkar kwallon kafa a Afirka, kuma a wannan gasar dake karewa yau, sun fito ne daga rukuni guda.

'Yan wasan Cote d'Ivoire
'Yan wasan Cote d'Ivoire AFP - FRANCK FIFE

A karawar da suka yi a wasan rukuni, Najeriya ta samu nasara a kan Cote d'Ivoire, abinda ya jefa kasar cikin mummunar yanayin da ta kori mai horar da 'yan wasan ta, yayin da ta tsallake rijiya da baya zuwa zagae na biyu.

Masana harkar kwallon kafa na hasashen cewar karawar ta yau zata fi ta farko da suka yi zafi, lura da cewar wanda ya samu nasara a yau shi zai dauki kofin gasar baki daya. 

Najeriya na hankoron samun nasara domin shiga jerin kasashen da suka lashe kofin har sau 4, yayin da kasar Cote d'Ivoire ke neman lashe kofin a karo na 3. 

Najeriya dai ta lashe wannan kofin ne a shekarar 1980 da 1994 da kuma shekarar 2013.

Kaftin Trust-Ekong na yi wa Allah godiya bayan samun nasara
Kaftin Trust-Ekong na yi wa Allah godiya bayan samun nasara © AFP

Idan Najeriya ta samu nasarar lashe kofin a yau, kaftin din ta Ahmed Musa da Kenneth Omerou za su zama 'yan wasan kasar guda 2 kacal da da suka taba lashe kofin har sau biyu, lura da cewar suna cikin tawagar 'yan wasan Super Eagles na shekarar 2013 da suka lashe kofin a karkashin jagorancin Stephen Keshi, kaftin din Najeriya da ya lashe kofin a shekarar 1994.

Tawagar 'yan wasan 1994 dake karkashin kaftin Keshi ne suka fara kai Najeriya gasar cin kofin duniya.

Masu sharhi a kan harkokin kwallon kafa na gabatar da hasashe daban daban a kan yadda suke kallon karawar ta yau wadda ake ganin zata dauke hankalin duniya.

Wasu daga cikin masu sharhin na bayyana goyan bayan da Cote d'Ivoire ke da shi a gida, lura da cewar a Abidjan za'a yi karawar a matsayin abinda zai bata kaimin samun nasara, yayin da wasu kuma ke cewa kwarewa da kuma sa'a shi zai taimakawa kasar da zata samu nasara.

Yanzu haka duk masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a Afirka sun yiwa Abidjan tsinke domin ganin yadda wasan zata kaya, cikin su harda shugabannin kwallon kafa ta duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.