Isa ga babban shafi
AFCON

Osimhen ya murmure zai iya buga wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

Likitocin da ke kula da tawagar ‘yan wasan Super Eagles, sun ce Victor Osimhen dan wasan gaba na tawagar zai buga wasan gobe da za su yi da Afrika ta Kudu.

Likitocin da ke kula da tawagar ‘yan wasan Super Eagles, sun ce Victor Osimhen zai iya buga wasan gobe da za su yi da Afrika ta Kudu.
Likitocin da ke kula da tawagar ‘yan wasan Super Eagles, sun ce Victor Osimhen zai iya buga wasan gobe da za su yi da Afrika ta Kudu. AFP - FRANCK FIFE
Talla

A Talatar nan ce dai Osimhen ya bar binin Abidjan don isa Bouake, inda za a buga wasan kusa da na karshe a gasar lashe kofin Afrika AFCON a gobe Laraba.

An dai fara tan-tama kan lafiyar dan wasan ne a jiya Litinin, bayan da tawagar ta fidda wata sanarwa da ke cewar dan wasan baya jin dadin jikinsa.

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles dai ta bar Osimhen a Abidjan don ci gaba da duba lafiyarsa, kafin daga bisani dan wasan ya bi sauran abokan wasansa zuwa Bouake.

Tun bayan faro gasar ta AFCON dai, kwallo daya ce gwarzon dan wasan Afrika ya jefa a raga, amma ya taimaka wa tawagarsa wajen samu nasara musamman a wasan da suka yi da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.