Isa ga babban shafi
AFCON

Za mu bada mamaki a karawarmu da Super Eagles - Hugo Broos

Mai horas da tawagar Afrika ta Kudu Hugo Broos, ya ce tawagar da yake jagoranta ta zaku ta ganta a wasan karshe na gasar AFCON.

Mai horas da tawagar Afrika ta Kudu Hugo Broos.
Mai horas da tawagar Afrika ta Kudu Hugo Broos. AFP - SIA KAMBOU
Talla

Tawagar da Bafana Bafana dai zata barje gumi ne da Super Eagles ta Najeriya a ranar Laraba mai zuwa, a matakin kusa dana karshe na gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

Tawagar ta samu nasarar kaiwa wannan matakin ne bayan da ta cire Cape Verde a wasan matakin dab da na kusa da na karshe da suka yi a ranar Asabar, a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Ana ganin tawagar Super Eagles a matsayin wacce tafi damar lashe wannan karawa da za su yi.

Toh amma a cewar mai horaswan dan asalin kasar Belgum da ya jagoranci tawagar Kamuru wajen lashe gasar a shekarar 2017, a shirye suke su  dakatar da Super Eagles a wannan wasa da za suyi.

 

“Wata kila mu bada mamaki a karawarmu da Najeriya, muna cike da yunwar buga wasan karshe a ranar Lahadi”

Sau daya ne dai tawagar Bafana Bafana ta taba samun nasara a kan Super Eagles a wasannin gasar AFCON, ita kuma ta samu nasara sau 2 sai kuma kunnen doki 3 da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.