Isa ga babban shafi

Ministan Isra'ila ya roki gafarar Biden bayan dansa ya kira shi da mai cutar mantuwa

Ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya fito ya roki gafarar Anurka game da sakon da dansa ya wallafa a shafin sada zumunta da ke bayyana shugaba Joe Biden a matsayin mai fama da cutar mantuwa.

Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir.
Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir. AP - Abir Sultan
Talla

Shuvael Ben-Gvir a wani sakonsa da ya wallafa a shafin X da aka fi sani da Twitter, ya sanya hoton Joe Biden tare da yin rubutu a saman hoton da ke cewa, "ya na da muhimmanci a wayar da kai game da yanayin matsalar kwakwalwa wanda ba sabon abu ba ne ga masu yawan shekaru".

Sakon dai kai tsaye na nufin Joe Biden mai shekaru 81 wanda ke shirin sake tsayawa takara a babban zaben Amurka da ke tafe a bana.

Duk da cewa Shuavael ya goge sakon nasa daga bisani, amma mahaifinsa ya sake amfani da kafar ta Twitter wajen mika sakon neman yafiya ga wadanda abin ya shafa.

Ministan tsaron na Isra’ila ya bayyana sakon dan nasa a matsayin babban kuskure, ya na mai bayyana Amurka a matsayin babbar kawa ga Isra’ila kuma Biden a matsayin mutum mai matukar muhimmanci.

Tun gabanin sakon Shuavael a baya-bayan nan anga yadda Ben-Gvir da kansa ke caccakar Biden bisa zarginsa da gaza bai wa Isra’ila gudunmawar da ta ke bukata a yakin da ta ke a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.