Isa ga babban shafi

Biden ya sha alwashin kai hare-hare Jordan don daukar fansar Sojin Amurka 3

Shugaba Joe Biden ya tabbatar da shirin Amurka na kai hare-hare Jordan da nufin daukar fansar kisan Sojojinta 3 da aka yi ta hanyar kai hari sansaninsu da jirgi marar matuki a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaba Joe Biden na Amurka.
Shugaba Joe Biden na Amurka. AP - Andrew Harnik
Talla

A jawabinsa gaban taron manema labarai bayan ziyartar iyalan sojojin 3 da suka mutu a jiya Talata, Joe Biden ya ce bayyana cewa Amurka za ta dauki fansar harin na karshen mako, duk da cewa baiyi karin haske kan lokacin da za su kai harin ba.

Harin na ranar Lahadi dai shi ne karon farko da Sojin Amurka ya rasa ransa tun bayana faro yakin Isra’ila a Gaza da ya birkita tsaro da zaman lafiyar gabas ta tsakiya.

Baya ga Sojin 3 da suka mutu rahotanni sun ce wasu gommai sun jikkata, lamarin da Joe Biden ke cewa sam ba batu ne da Amurka za ta lamunta ba.

A cewar Biden Amurka za ta mayar da martini mai zafi wanda zai kange duk wani yunkurin sake kaiwa sansaninta hari ba kadai a kasar ta Jordan ba har da sauran sansanoninta da ke gabas ta tsakiya.

Akwai dai fargabar martanin Amurka ya sake dawo da tashe-tashen hankulan da aka shafe shekaru ana fama da shi a iyakar Jordan da Syria.

Amurka dai ta dora alhakin harin na ranar Lahadi kan mayakan kungiyoyin yankin na gabas ta tsakiya yayinda Iran ta nesanta kanta da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.