Isa ga babban shafi

Biden ya sha alwashin daukar fansa kan kisan dakarun Amurka a Jordan

Harin jirgi mara matuki da aka kai wani sansanin soji a Jordan ya yi sanadin mutuwar dakakrun Amurka 3, tare da jikkata wasu sama da 30 a ranar Lahadi, harin da shugaban Amurka Joe Biden ya dora alhakinsa a kan ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, inda ya sha alwashin mayar da martani.

Shugaban Amurka, Joe Biden.
Shugaban Amurka, Joe Biden. © AP/Matt Rourke
Talla

Wannan ne karo na farko da aka kashe sojojin Amurka ta wannan hanyar a Gabas ta Tsakiya, tun da yaki ya barke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu, kuma wanna lamari ka iya ta’azzara tankiya a yankin, tare da tsoron fadadar rikicin.

Sanarwar da ta fito daga fadar shugaba Biden ta ce ana nan ana gudanar da binciken gaskiyar lamari a kan harin, wanda Biden ya ce ya san mayakan Houthi ne suka aiwatar da shi.

A daidai lokacin da ake fargabar bazuwan wannan rikici a Gabas ta Tsakiya, sakamakon yakin da ake tsakanin Isra’ila da  Hamas a Gaza, mahukuntan Amurka sun lura cewa daya daga cikin dimbim kungiyoyin da Iran ke mara wa baya ne suka kai wannan hari, sai dai har yanzu ba su kai ga gano ainihin kungiyar ba.

Iran ta musanta wata nasaba da wannan hari da ya rutsa da dakarun Amurka, ta wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar  harkokin wajenta  a  Litinin din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.