Isa ga babban shafi

'Yan Houthi sun harba makami mai linzami kan jirgin yakin Amurka

'Yan tawayen Houthi na Yemen sun harba makami mai linzami kan jirgin ruwan yakin Amurka da ke sintiri a mashigin tekun Aden a ranar Juma'a, lamarin da ya tilastawa jirgin mayar da martani.

Jirgin ruwan yakin Amurka
Jirgin ruwan yakin Amurka AP - Mass Communication Specialist Seaman Anna Van Nuys
Talla

Harin da aka kai kan jirgin ruwan yakin Amurka, Amurka USS Carney, ya nuna wani sabon tashin hankali a fada mafi girma da sojojin ruwan Amurka suka yi a yankin gabas ta tsakiya cikin shekaru da dama da suka gabata,a daya gefen 'yan tawayen Houthi sun kai wani harin makami mai linzami wanda ya kona wani jirgin ruwan kasuwanci a cikin dare daga ranar Juma’a zuwa jiya Asabar.

Harin yan tawayen Houthi kan wani jirgin kasuwanci
Harin yan tawayen Houthi kan wani jirgin kasuwanci AP

Da sanyin safiyar jiya Asabar, sojojin Amurka sun kai wani hari kan wani makami mai linzami na Houthi.

'Yan tawayen Houthi
'Yan tawayen Houthi AP

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta tauraron dan adam ta Houthis ta ce an kai harin ne a kusa da birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa, ba tare da bayar da bayyanai dangane da barnar da aka samu biyo bayan hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.