Isa ga babban shafi

Iran ta nesanta kanta da hannu a harin da ya kashe sojin Amurka 3

Iran ta nesanta kanta da hannu a harin jirgi marar matukin da ya kashe Sojin Amurka 3 tare da jikkata wasu da dama a Jordan jiya Lahadi, harin da tuni ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya tsakanin manyan kasashe.

Harin jirgi marar matukin ya kashe akalla Soji 3 tare da jikkata wasu da dama.
Harin jirgi marar matukin ya kashe akalla Soji 3 tare da jikkata wasu da dama. AP
Talla

Shugaba Joe Biden na Amurka da sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron sun dora alhakin harin na jiya Lahadi kan kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ruwaito kakakin ma’aikatar Nasser Kanaani na cewa kungiyoyin da ke yanking abas ta tsakiya na mayar da martini ne kan kisan kare dangin da Yahudawa ke yiwa ‘yan uwansu a Gaza, amma ba Iran ke basu umarnin aikata hakan ba.

A cewar sanarwar wadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya wallafa, kungiyoyin na yin gaban kansu ne wajen aikata abin da suke ganin ya dace gwargwadon tsare-tsarensu da kuma manufofinsu.

A cewar Kanaani aikin da Iran ke yi kadai shi ne bayar da kwarin gwiwa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankin na gabas ta tsakiya wanda Isra’ila ke ci gaba da wargazawa.

Harin wanda aka kai jiya Lahadi da jirgi marar matuki kan sansanin sojin na Amurka shi ne karon farko da Amurkan ke rasa Soji tun bayan faro kisan kare dangin Isra’ila a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.