Isa ga babban shafi

Kotu ta umurci Trump ya biya dala miliyan 83 ga E. Jean Carroll saboda bata mata suna

A jiya Juma’a wata kotu a birnin New York ta umarci tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya biya dala miliyan 83.3 ga marubuci E. Jean Carroll bisa zargin bata mata suna a shekarun 1990.

: E. Jean Carrol yan lokuta bayan zaman kotu a New York
: E. Jean Carrol yan lokuta bayan zaman kotu a New York REUTERS - BRENDAN MCDERMID
Talla

Alkali a birnin New York na kasar Amurka ya umarci tsohon shugaban kasar Amurka kuma dan takara a zaben 2024 Donald Trump da ya biya dala miliyan 83.3 domin biyan mawallafin E. Jean Carroll diyya, wanda aka same shi da yin lalata da kuma bata mata suna.

A wanan zama na kotu,Trump ya yi kakkausar suka, inda ya kira hukuncin a matsayin abin dariya a wata sanarwa da ya yi tare da yin alkawarin daukaka kara.

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS - MIKE SEGAR

Alkalan kotun sun cimma matsaya ne bayan tattaunawa da suka yi kasa da sa'o'i uku.

Trump ya kasance a gaban kotu tun da farko, yana yin katsalandan a lokaci guda,ya kuma fic daga zauren amma daga baya ya dawo don rufe muhawara.

Jean Carrol, mace dake zargin Donald Trump da bata mata suna
Jean Carrol, mace dake zargin Donald Trump da bata mata suna AP - Seth Wenig

"Wannan babbar nasara ce ga duk macen da ta tashi tsaye lokacin da aka yi mata rauni.

Umurnin ya ƙunshi dala miliyan 65 na diyya bayan alkalan kotun sun gano cewa Trump ya aikata mugunta a yawancin maganganunsa na jama'a game da Carroll, dala miliyan 7.3 na diyya da dala miliyan 11 don shirin gyara suna.

Lauyan Trump Alina Habba ta ce "an cire mana duk wata kariya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.