Isa ga babban shafi

Karon farko a shekaru 40 Amurka ta zartas da kisa ta hanyar amfani da iska mai guba

Mahukuntan jihar Alabama a Amurka sun aiwatar da hukuncin kisa kan Kenneth Smith ta hanyar amfani da hayaki mai guba na Nitrogen, wanda ke matsayin karon farko da aka taba amfani da salon hukuncin cikin fiye da shekaru 40 bayan gabatar da shi a kasar.

Salon kisan kan ta hanyar amfani da guba akan yiwa mutum allurar iskar ta Nitrogen ne wadda za ta lalata sassan jiki tare da zagwanyar da mutum cikin sa'o'i 30.
Salon kisan kan ta hanyar amfani da guba akan yiwa mutum allurar iskar ta Nitrogen ne wadda za ta lalata sassan jiki tare da zagwanyar da mutum cikin sa'o'i 30. AP - DAVE MARTIN
Talla

Tun a jiya Alhamis ne aka faro hukuncin kisan ta hanyar amfani da hayakin na Nitrogen kan Kenneth Smith mai shekaru 58 wanda ya aikata laifin kisan kai a shekarar 1988 lokacin da ya yi kisan gilla ga wata mata mai suna Seneth, kuma tun daga wancan lokaci ne ya aka zartar massa da hukuncin kisan wanda ba a kai ga aiwatarwa ba sai a yanzu.

Salon hukuncin kisan wanda Amurka ta gabatar da shi a shekaru 40 da suka gabata, akan yi allurar iskar mai guba ne wanda sannu a hankali take bin jikin bil’adama gabanin kashe shi cikin as’o’i 30.

Gabanin aiwatar da hukuncin wanda ya kai ga kisan na Kenneth a yau Juma’a, lauyoyin da ke kare makashin sun bukaci sauya salon aiwatar da hukuncin wajen amfani da saukakkar hanyar kisan mai laifin, amma mahukuntan na jihar Alabaman Amurka suka kafe wajen ganin lallai na aiwatar da hukuncin kamar yadda kotu ta umarta.

Wannan dai shi ne karon farko da Amurka ke amfani da salon wanda kuma ya gamu da kakkausar suka daga masu fafutukar kare hakkin dan adam da ke kallonshi a matsayin tsantsar rashin tausayi lura da tsawon lokacin da ya ke dauka yana narka halittun dan adam gabanin kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.