Jirgin saman Sakataren harkokin wajen Amurka Blinken ya lalace a Zurich
Duniya – Jirgin saman dake zirga zirga da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a kasashen duniya, ya lalace a Zurich dake kasar Switzerland, saboda abinda aka kira tsiyayar iskar da aka samu, abinda ya tilasta tura wani jirgi na daban domin mayar da shi Washington.
Wallafawa ranar:
Blinken wanda shine babban jami’in diflomasiyar Amurka, ya ziyarci Davos ne wajen taron tattalin arziki na duniya da ake gudanarwa kowacce shekara, yayin da aka shirya cewar a yau laraba ya kamata ya koma gida.
Bayan kammala halartar taron Davos, Blinken ya hau jirgin sama mai saukar ungulu zuwa Zurich dan amfani da babban jirgin sa zuwa Washington, amma sai aka gano jirgin na da matsala, saboda haka ba zai iya tashi zuwa Washington ba.
Rahotanni sun ce anyi amfani da wani jirgi na daban domin daukar Blinken zuwa gida, yayin da aka umarci ‘yan tawagar sa da kowa ya nemi hanyar komawa gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu