Isa ga babban shafi

Akwai bukatar Isra'ila ta taimaka wa gwamnatin yankin Falasdinu

A sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi kira ga Isra’ila da ta taimaka wa mahukuntan Falasdinu a maimakon dakile su, yana mai cewa makomar tsaron Isra’ila ya ta’allaka ne a kan hakan.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken tare da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a garin Ramallah. 10 ga Janairun, 2024.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken tare da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a garin Ramallah. 10 ga Janairun, 2024. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Da ya ke jawabi a taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a birnin Davos, Blinken ya sabunta kiransa na samar da kasar Falasdinu, duk da cewa Amurka tana goyon bayan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza, biyo bayan farmakin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Sakataren harkokin wajen na Amurka ya shaida wa Isra’ila cewa ba za ta samu ingantaccen tsaro da ta ke bukata ba idan babu ingantacciyar hukumar Falasdinu da za ta kyautata wa al’ummarta.

Amurka dai na ci gaba da nanata goyon bayan Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a game da aniyarsa ta kawar da kungiyar Hamas, wadda ke jagorancin Zirin Gaza, sai dai ta bayar da shawarar bai wa mahukuntan Falasdinu, a karkashin jagorancin Mahmud Abbas damar karbar ragamar jagorancin Zirin sannu a hankali.

Hare-haren Isra’ila sun kassara Zirin Gaza tun bayan ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu 24, kashi 70  daga cikinsu mata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.