Isa ga babban shafi

Isra’ila ta kai hari kan tawagar motocin kayan agaji akan hanyar Gaza

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar yankin Falasdinu, ya ce Sojojin Isra’ila sun kai hari kan tawagar motocin da ke aikin rarraba kayakin agaji akan hanyarsu ta dawowa daga Gaza.

Al'ummar Gaza na cikin matsanancin karancin abinci da ruwan sha bayan katse hanyoyin da ke samar musu ruwa da kuma hana shigar da kayakin agaji yankin.
Al'ummar Gaza na cikin matsanancin karancin abinci da ruwan sha bayan katse hanyoyin da ke samar musu ruwa da kuma hana shigar da kayakin agaji yankin. via REUTERS - JORDANIAN ARMED FORCES
Talla

Sanarwar da ofishin ya wallafa a shafinsa na X dauke da sa hannun Tom White babban daraktan ofishin, ya ce babu ko mutum guda da ya jikkata, sai dai motocin sun samu illa matuka.

A cewar Mr White, tawagar motocin na wucewa ne ta hanyar da ke gab da inda Sojojin Isra’ila suka girke makamansu a gab da zirin na Gaza, wanda tilas suka dakatar da tafiyar ta su.

Zuwa yanzu alkaluman Falasdinawan da Isra’ila ta kashe ya tsamma dubu 22 tun bayan faro kisan kare dangin da ta ke yiwa larabawan a ranar 7 ga watan Oktoba.

Haka zalika Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wajen tsira a yankin na Gaza lura da yadda Isra’ilan Yahudu ke ci gaba da farmakar kowanne lungu da sako dai dai lokacin da yankin ke ci gaba da fama da rashin ruwa da wuta dama abinci.

Isra'ila ta rushe fiye da kashi 2 bisa 3 na yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.