Isa ga babban shafi
Yakin Gaza

Isra'ila ta bada umarnin kwashe jama'a daga kudancin Gaza

Isra’ila ta bada umarnin kwashe karin jama’a daga yankin kudancin Gaza a daidai lokacin da jami’an diflomasiyya suka matsa kaimi wajen ganin an dakatar da yakin da kungiyar Hamas ta ce, ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 20.

Kimanin mutane dubu 140 ne ke samun mafaka a yankin kudancin Gaza bayan sun rasa muhallansu a sanadiyar yakin.
Kimanin mutane dubu 140 ne ke samun mafaka a yankin kudancin Gaza bayan sun rasa muhallansu a sanadiyar yakin. REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a jiya Laraba ne Isra’ilar ta bada umarnin kwashe jama’ar  daga wasu yankuna masu fadi da ke birnin  Khan Yunis, inda sama da mutane dubu 140 ke samun mafaka bayan sun rasa muhallansu.

A lokacin da yakin ke farko-farko, Isra’ila ta shaida wa fararen hula da su fice daga yankin arewacin Falasdinu da aka yi wa kawanya, tana mai kira a gare su da su nemi mafaka a yankunan da ke kudanci.

Sai dai a yanzu, wuraren da jama’a ke neman mafaka a cikinsu sun yi karanci, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da fusata sakamakon karuwar alkaluman mamata.

Ofishin Yada Labarai na gwamnatin Hamas da ke Zirin Gaza ya bayyana cewa, akalla mutane dubu 20 ne aka kashe a yankin na Falasdinu tun bayan barkewar yakin da Isra’ila.

Hamas ta ce, akwai kananan yara dubu 8 da mata dubu 6 da 200 da suka rasa rayukansu a wannan yakin wanda aka fara shi a ranar 7 ga watan Oktoba bayan wani hari da Hamas ta kaddamar cikin Isra’ila da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.