Isa ga babban shafi

Iran da Rasha sun kulla yarjejeniyar kasuwanci da kudadensu maimakon dalar Amurka

Iran da Rasha sun kammala yarjejeniyar kasuwanci da kudaden kasashensu maimakon dalar Amurka.

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan, tare da shugaban Iran, Ebrahim Raisi.
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan, tare da shugaban Iran, Ebrahim Raisi. © AFP
Talla

Sanarwar da bangarorin biyu suka fitar yayin wani taron ganawa da gwamnonin manyan bankunan kasashen biyu suka yi a kasar Rasha, sun ce hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikinsu a fannini da dama.

Duka dai kasashen Iran da Rasha na fuskantar takunkumin Amurka da sauraan kasashen yammacin duniya.

"Bankuna da ‘yan kasuwa, a yanzu za su iya amfani da ababen more rayuwa ciki har da tsarin bankunan da ba na SWIFT ba don mu'amala da kudaden cikin gida," in ji kafofin yada labarai na gwamnati.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, mambobin kungiyar bunkasa Tattalin Arzikin yankin Asiya karkashin jagorancin Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya da Iran a ranar 25 ga watan Disamba.

Iran ta kara zama mai muhimmanci ga fadar Kremlin bayan takunkumin da kasashen yammacin Turai suka kakaba mata kan rikicin Rasha a Ukraine wanda ya takaita harkokin kasuwancin kasashen waje ga Rasha tare da tilasta mata neman kasuwanni a wajen Turai.

Hukumomin Iran sun ce hadin gwiwar soji da Rasha na kara fadada, yayin da ta ce, ta kammala shirye-shiryen karbar jiragen yakin Su-35, jirage masu saukar ungulu na Mi-28 da kuma jirgin horar da matukan jirgi da ake kira da Yak-130 daga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.