Isa ga babban shafi

Iran ta bai wa Mata damar kallon wasan sada zumunta tsakaninta da Rasha

Iran ta bai wa magoya baya mata damar shiga filin wasa don kallon wasan sada zumuntar da kasar ta doka tsakanin ta da Rasha, karon farko cikin fiye da shekara guda da matan ke samun irin wannan dama.

Mata a Iran na tsananin son kallon wasa yayinda mahukuntan kasar ke ci gaba da haramta musu.
Mata a Iran na tsananin son kallon wasa yayinda mahukuntan kasar ke ci gaba da haramta musu. AFP - ATTA KENARE
Talla

Wasan wanda ya gudana a filin wasa na Azadi da ke birnin Tehran, dandazon mata masoya kwallo sun samu damar shiga filin tare da karfafa gwiwa ga tawagar kasar wadda ta yi canjaras da Rasha da kwallo 1 da 1.

Rahotanni sun ce cikin matan da suka shiga filin wasan akwai wadanda suka shafe tafiyar nisan sa’o’I 12 gabanin shiga Tehran duk don kallon wasan na daren jiya.

Wasu daga cikin malaman addini a Iran har yanzu na ci gaba da kalubalantar shigar Mata filayen wasanni.
Wasu daga cikin malaman addini a Iran har yanzu na ci gaba da kalubalantar shigar Mata filayen wasanni. AP - Vahid Salemi

Ko a watan Maris din shekarar da ta gabata, sai da aka samu tashin hankali a kasar ta Iran bayan da mahukunta suka hana mata shiga kallon wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Duniya da kasar ta doka da Lebanon duk da yadda aka basu damar sayen tikiti, matakin da ke zuwa watanni 2 bayan baiwa mata damar kallon wasan Iran da Iraqi.

Tun bayan juya-juya halin da ya mayar da Iran daular musulunci a 1979, mahukunta kasar suka haramtawa mata shiga filayen wasa don kallo kwallo da sauran wasannin maza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.