Iran ta yarda ta aikewa Rasha kuraman jirage amma tace kafin yakin Ukraine ta yi
A karon farko kasar Iran ta amince cewa lallai ta aikewa Rasha jiragen yaki marasa matuka amma ta dage cewa ta yi hakan ne tun kafin mamayar Moscow a Ukraine.
Wallafawa ranar:
Ukraine da kawayenta na Yamma sun sha zargi Rasha da yin amfani da jirage marasa matuka da Iran ta kera a 'yan makonnin nan wajen kai hare-hare a kan Ukraine.
Tehran dai ta sha musanta wannan ikirari amma a wannan Asabar, wasu majiyoyi sun jiyo ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian na cewa an aike da jirage marasa matuka zuwa Rasha ne kafin fara kai farmakin a karshen watan Fabrairu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Amir-Abdollahian na cewa, "Mun baiwa kasar Rasha wasu takaitaccen adadi na jirage marasa matuka watanni kafin yakin Ukraine."
Makwanni da dama, sojojin Rasha sun yi ruwan bama-bamai da makamai masu linzami a kan ababen more rayuwa na Ukraine, yayin da wani gagarumin farmakin da kasar Ukraine ke kai wa ta kasa da taimakon makaman kasashen yammacin duniya -- ya tilastawa sojojin Rasha ja da baya a wasu yankuna da ta mamaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu