Isa ga babban shafi

Zelensky ya zargi Rasha da sake sayo jirage marasa matuki daga Iran

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasar Rasha ta yi odar jirage marasa matuka kimanin dubu 2,000 daga Iran, irin wadanda dakarun Moscow suka yi amfani da su, wajen kai hare-hare a sassan kasar ta Ukraine a baya-bayan nan.

Shugaba Volodymyr Zelensky yayin jawabin kai tsaye ga al'ummar Ukraine.
Shugaba Volodymyr Zelensky yayin jawabin kai tsaye ga al'ummar Ukraine. AP - Ludovic Marin
Talla

Zelensky ya bayyana haka ne, yayin jawabi a wani taro da jaridar Haartz ta Isra’ila ta shirya, inda ya ce kullum sai an ji mummunar karar jiragen Iran marasa matuka a sararin samaniyar Ukraine cikin dare.

Sai dai shugaban bai fayyace cewa ko jiragen marasa matuka da ya ke magana a kansu, sabbi ne da Rasha ta yi oda daga Iran ba, ko kuma wadanda ta riga ta saya ne tun a baya.

Amurka da Turai sun yi imanin cewa da jiragen marasa matuka samfurin Iran ne Rasha ke kaddamar da hare-haren baya-bayan nan a Ukraine dalilin da ya sanya su sake kakabawa Tehran takunkumai kan taimakawa Moscow da makami.

Tun bayan harin da ya karya gadar Kerch wadda Rasha ta gida da ya hadeta da yankin Crimea ne, kasar ta zafafa hare-hare a sassan birnin Kiev da kewaye wanda bayanai ke cewa ya haddasa asarar dimbin rayuka ciki har da fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.