Isa ga babban shafi

Yakin Ukraine: Turkiyya ta zargi Amurka da kokarin shafawa Saudiyya kashin kaji

Turkiyya ta zargi Amurka da watsawa Saudiya kasa a ido, bayan da kungiyar OPEC da kawayenta suka sanar da rage yawan man da suke hakowa duk da adawa da hakan da Amurkan ta yi.

Shugaban Turkiyya kenan, Recep Teyyip Erdogan.
Shugaban Turkiyya kenan, Recep Teyyip Erdogan. REUTERS - BRENDAN MCDERMID
Talla

Kungiyar OPEC ta sanar a baya-bayan nan cewa za ta samar da gangar mai miliyan biyu kasa da kowace rana daga watan Nuwamba, wanda zai hana wadatar da shi a kasuwar da ta riga ta shiga tsaka mai wuya, duk da matsin lamba daga Amurka da sauran kasashen duniya na kara hakowa.

A makon da ya gabata ne, shugaban Amurka Joe Biden ya bayana cewa akwai matakan da kasarsa za ta dauka kan Saudiyya, bayan matakin da OPEC da kawayenta suka yanke.

“Mun ga cewa wata kasa ta yi wa Saudiyya barazana, musamman a kwanan baya. Wannan cin zarafn ba daidai ba ne," in ji ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu a wani taron manema labarai da ya gudanar a  kudancin Turkiyya ranar Juma'a.

"Muna ganin bai dace Amurka ta yi amfani da wata kalma da ke a matsayin wani bangare na matsin lamba kan Saudiyya ko wata kasa ba."

Amurka na bukatar Saudiyya da kawayenta na kungiyar OPEC sun kara fitar da mai don taimakawa wajen rage tsadar man fetur da kuma saukaka hauhawar farashin kayayyaki a Amurka.

Sai dai kungiyar OPEC mai mabobi irin su Saudiyya da kuma karin wasu kasashe masu samar da mai 10 karkashin jagorancin Rasha sun yanke shawarar rage yawan man da ake hakowa a duniya a wata mai zuwa.

Ana sa ran matakin zai haifar da hauhawar farashin man fetur, wanda zai taimakawa Rasha matuka.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya ce matakin na OPEC da kawayenta, na yadda za a inganta tattalin arziki ne kawai kuma kasashe mambobinta sun dauki matakin bai daya.

Masarautar Saudiyya, ta kuma musanta cewa tana daukar bangare kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine mai samun goyon bayan kasashen Yamma, tana mai nanata cewa ta ci gaba da kasancewa "matsayi mai ka'ida" na goyon bayan dokokin kasa da kasa.

Ministan tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman, ya ce ya yi mamaki zargin da ake yi kasarsa na cewa kai tsaye tana goyon bayan yakin da Rasha ke yi a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.