Isa ga babban shafi

Wani magidanci ya kashe 'yayansa hudu tare da matarsa a Faransa

‘Yan sanda a Faransa, sun cafke wani magidanci da ake zargi da amfani da wuka wajen kashe matarsa da yaransa hudu a ranar bikin Kirismeti.

Iyalai da abokai na ci gaba da zuba furanni a wajen gidan da aka gano gawawwakin yara da matar da ke birnin Paris.
Iyalai da abokai na ci gaba da zuba furanni a wajen gidan da aka gano gawawwakin yara da matar da ke birnin Paris. REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Masu bincike sun ce. An gano gawawwakin iyalan nasa cikin jinni a wani gida da ke Meaux, kilomita arba’in tsakanin wurin da arewa maso gabashin birnin Paris.

Mai shigar da kara, Jean-Baptiste Bladier, ya ce matar da ‘yayanta mata guda biyu a daddaba musu wuka, sannan ba za a iya fayyace irin bugun da suka sha a hannunsa ba, inda aka ake zargin sauran yara biyun an shake musu wuya ne ko kuma danna kansu a cikin ruwa.

‘Yan sanda dai na ci gaba da tsare mutumin mai shekaru 33, inda aka fara gudanar da binciken kisan kai a kansa.

Yaran ‘yan tsakanin watanni tara da kuma masu shekaru 10, makota sun shaidawa masu bincike cewa sun jiyo ihunsu da sanyin safiyar ranar Kirismeti.

Daga bisani ne aka mika rahoton faruwar hakan zuwa ofishin jami’na tsaro, bayan rashin samun bayanan abin da ke faruwa da su.

Rahotanni ssun ce, mijin matar ya taba samun matsalar tabin hankali a shekarar 2019, inda a lokacin ya taba cin zarafin matar tasa da wuka, kuma a wancan lokacin ta kaucewa gurfanar da shi gaban shari’a saboda matsalar da yake fama da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.