Isa ga babban shafi

Sama da Falasdinawa dubu 20 ne suka rasa rayukansu a rikicin Hamas da Isra'ila

Ma’aikatar lafiyar Gaza ta ce adadin Falasdinawan da suka rasa rayukansu a sanadiyar rikicin Hamas da Isra’ila ya kai dubu 20 da dari 424, tun bayan faro rikicin a ranar 7 ga watan Oktoban wannan shekarar.

Sama da Falasdinawa dubu 20 ne suka mutu a yakin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila.
Sama da Falasdinawa dubu 20 ne suka mutu a yakin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila. © Ibraheem Abu Mustafa / Reuters
Talla

Wannan adadi ya hada da mutane 166 da suka rasa rayukansu a cikin sa’oi 24 suka gabata a yankin Gaza.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra’ila ta ce tayi asarar sojoji 153, tun bayan da suka kaddamar da yaki ta kasa a Gaza, a ranar 27 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra'ila dauke da gawar daya daga cikin abokan aikinsu da aka kashe a yankin Gaza.
Sojojin Isra'ila dauke da gawar daya daga cikin abokan aikinsu da aka kashe a yankin Gaza. REUTERS - VIOLETA SANTOS MOURA

Ko a jiya Asabar sai da Isra’ila ta rasa sojoji 10, adadi mafi yawa da kasar ta taba rasawa a rana guda a wannan yaki da take yi.

A cikin wata sanarwa da fara ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar ya jajantawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu.

"Yakin nada wuya sosai, amma bamu da zabi face ci gaba da gwabza fada har sai mun mun samu nasara, sai mun cimma burinmu".

Sanarwar ta Netanyahu ta ambatoshi inda ya ke shan alwashin kare rayukan sojojinsu da ke fagen daga.

 

 

.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.