Isa ga babban shafi

Kwamitin Tsaron MDD na shan caccaka kan kudurinsa a Gaza

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam, da na agaji da sauran masu fafutuka da kuma wasu kasashe, sun bayyana bacin ransu kan gazawar da suka ce Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake yi wajen kawo karshen tashin hankalin da Falasdinawa ke ciki a Zirin Gaza.

Zauren Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya
Zauren Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya REUTERS - DAVID DEE DELGADO
Talla

A ranar Juma’a, kwamitin sulhun ya zartas da kudurin da ya bukaci shigar da karin agaji zuwa Gaza, ba kuma tare da yin kira kai tsaye da a tsagaita bude wuta a yakin Isra'ila da Hamas ba, lamarin da ya fusata bangarori da dama, ciki har da wadanda ke ganin kiris ya rage su bayyana kudurin a matsayin maras ma’ana.

An dai cimma matsaya kan kudurin ne bayan dage zama sau da dama da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniyar yayi domin laluben tsarin da zai bi wajen gabatar da abinda Amurka ba za ta sake yin watsi da shi ba, kamar yadda ta rika yi a baya kan yakin na Isra’ila a Gaza.

Kudurin ya samu amincewar kuri'un kasashe 13 masu kujerar dindindin, yayin da Amurka da Rasha suka kauracewa jefa nasu kuri’un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.