Isa ga babban shafi

Yadda sabuwar dokar Faransa ta shafi daliban Najeriya

Majalisar Dokokin Faransa ta zartar da dokar hana daliban kasashen waje, ciki kuwa har da Najeriya shigo da iyalansu kasar.

Faransa ta ce dalibai kan yi amfani da damar da ake basu wajen shiga kasar da iyalansu.
Faransa ta ce dalibai kan yi amfani da damar da ake basu wajen shiga kasar da iyalansu. © Dailytrust
Talla

Wannan mataki dai ya samu goyon baya daga jam'iyyar Renaissance ta shugaba Emmanuel Macron da kuma Jam’iyyar National Rally ta Marine Le Pen.

Manufofin shige da ficen da aka yi wa kwaskwarima na tsaurara matakai kan ziyarar dangin dalibai, ta hana bakin haure damar samun walwala, da kuma haramta tsare yara kanana a wuraren tsare manyan mutane.

Sai dai kuma shugabanni daga kashi daya bisa uku na yankunan Faransa sun bayyana kin aiwatar da wasu muhimman matakai na wannan doka.

Kudirin da aka yi wa kwaskwarima, mafi tsauri na kudirin ya samu goyon bayan jam’iyyun masu tsatssauran ra’ayi, wanda ya kai ga amincewa da shi kwanan nan.

Le Pen ta yaba da sauyin matakin tana me bayyana hakan matsayin nasara ta akida ga masu ra'ayin mazan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.