Jirgin ruwan sojojin Faransa mai suna Mistral wanda tsayinsa ya kai mita 200 da ke da nauyin kusan Tan 22,000, dauke da jiragen ungulu na yaki 16, ya shiga ruwan Najeriya, domin halartar atisaye hadin gwiwa da aka yiwa sunan Crodile Lift da Grand African Nemo, wanda aka fara a ranar 9 ga watan Oktoban 2023.
Atisayen zai mayar da hankali ne kan yaki da fataucin hodar iblis, satar fasaha, fataucin mutane, kamun kifi ba bisa ka'ida ba, da kuma fashin teku.
Gidan rediyon Faransa na RFI ya samu tattaunawa da Kyaftin din jirgin ruwan na Mystral.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu