Isa ga babban shafi

Shugaba Tinubu zai yi balaguronsa na farko

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai yi balaguronsa na farko a matsayin na shugaban kasar zuwa birnin Paris na Faransa a ranar Alhamis domin halartar taron nazari tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da kudade ga kananan kasashen duniya. 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mika gaisuwa da dandazon mahalarta bikin rantsar da shi a birrnin Abuja.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mika gaisuwa da dandazon mahalarta bikin rantsar da shi a birrnin Abuja. REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

Mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan yaada labarai da tsare-tsare, Dele Alake, shi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin.

Shugaba Tinubu zai samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatinsa zuwa wannan taron wanda zai gudana bayan fuskantar mummunan tasirin sauyin yanayi da matsalar karancin makamashi da kuma tasirin annobar Covid-19.

Za a gudanar da taron ne a Palais Brongniart karkashin jagorancin shugaba Emmanueel Macron na Faransa.

Shugaba Tinubu zai halarci taron na kwanaki biyu wanda zai mayar da hankali kan cike gurbin rashin kudi ga kasashe musamman matalauta da ke fuskantar kalubale daban-daban kamar na bashi da sauyin yanayi da kuma karancin masu zuba jari baya ga bunkasar tattalin arziki.

Shugaba Tinubu da sauran takwarorinsa na duniya da manyan kamfanonin kasa da kasa da masana harkokin kudade da masa tattalin arziki za su yi nazari mai zurfi kan yadda za a farfado da tattalin arzikin kananan kasashe da suka yi fama da tasirin annobar Covid-19 da kuma ke fuskantar tsananin  talauci 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.