Isa ga babban shafi

Arsenal ta koma saman teburin firimiya bayan doke Brighton

Duniya – Kungiyar kwallon kafar Arsenal tayi nasarar komawa saman teburin gasar Firimiya sakamakon nasarar da ta samu a kan Brighton da ci 2-0.

Kai Havertz na daga cikin wadanda suka jefawa Arsenal kwallo
Kai Havertz na daga cikin wadanda suka jefawa Arsenal kwallo AFP - IAN KINGTON
Talla

Gabriel Jesus da Kai Haverts suka jefawa Arsenal kwallayenta guda 2 a mintina 53 da 87, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ba tare da an jefa kwallo ba.

Wannan nasarar ta baiwa Arsenal damar samun karin maki 3, abinda ya kawo adadin makinta zuwa 39 daga wasanni 17 da tayi.

Yanzu haka kungiyar na matsayi na farko da maki 39, sai Aston Villa a matsayi na 2 da maki 38, sannan Liverpool a matsayi na 3 da maki 37, yayin da ita Liverpool take karawa da Manchester United yanzu haka.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi yau lahadi sun nuna cewar, Aston Villa ta doke Brentford da ci 2-1, sai kuma West Ham da ta doke Wolves da ci 3-0.

Ita kuwa West Ham ta na matsayi na 7 ne da maki 27.

Manchester City da ta tashi 2-2 da kungiyar Crystal Palace a ranar asabar na matsayi na 4 da maki 34.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.