An yi gwanjon rigunan da Messi ya saka a Qatar a kan dala miliyan 7 da rabi
Duniya – Yau anyi gudanar da gwanjon rigunan wasan da Lionel Messi na Argentina ya saka guda 6 a gasar cin kofin duniyar akayi bara a kasar Qatar, inda aka sayar da su a kan kudin da ya kai dala miliyan 7 da dubu 800 a birnin New York.
Wallafawa ranar:
Mutane 3 suka gabatar da tayi daban daban lokacin gwanjon da kamfanin Sotheby ya jagoranta na rigunan fitaccen ‘dan wasan wanda ya jagoranci kasarsa ta Argentina lashe kofin duniyar.
A karshe, an yi nasarar sayar da rigunan guda 6, abinda ya dada daga darajar Messi a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka fito daga kasar ta Argentina.
Messi ya jagoranci Argentina wajen doke kasar Faransa a bugun daga-kai-sai mai tsaron gida a kasar Qatar, domin lashe kofin duniyarsa ta farko a ranar 18 ga watan Disambar bara.
Brahm Wachter, shugaban kamfanin Sotheby da ya gudanar da gwanjon, yace gasar ta bara ta zama daya daga cikin mafi inganci a tarihin wasannin cin kofin duniyar da aka gani, tare da sake daga tauraron Messi a duniya.
Wachter yace sayar da wadannan riguna guda 6 na da matukar tarihi, tare da kusanto da wadanda suka yi nasarar saye kusa da nasarar Messi a gasar da ta gabata.
A farkon wannan wata, mujallar Times ta Amurka, ta bayyana Messi a matsayin gwarzonta na wannan shekarar ta 2023, bayan lashe kyautar Bllon D’Or a karo na 8, abinda ba’a taba gani ba a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu