Isa ga babban shafi

Falasdinawa sun mayar da kasuwa Makabarta saboda rashin wajen birne gawarwaki

Al’ummar yankin Gaza a Falasdinu sun mayar da kasuwar da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia zuwa makabarta, sakamakon shingayen da Isra’ila ta sanya ga yankin da zai kai su ga inda suke birne mamatansu.

Zuwa safiyar yau Laraba Isra'ila ta kashe fararen hular da yawansu ya kai dubu 18.
Zuwa safiyar yau Laraba Isra'ila ta kashe fararen hular da yawansu ya kai dubu 18. © REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Kasuwar na daga cikin yankunan da Isra’ila ta yi wa luguden wuta tare da kashe daruruwan fararen hula a hare-haren da ta ke ci gaba da kaiwa, inda ta rushe kusan dukkanin gine-ginen da ke cikinta.

Falasdinawan sun rika gina manyan kaburbura a cikin kasuwar tare da birne jama’arsu ta yadda suke sanya alama mai dauke da sunayen wadanda ke cikin kabarin don gujewa bacewarsu.

Zuwa safiyar yau Laraba Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 18 baya ga raba fiye da kashi 80 na yawan al’ummar Gaza miliyan 2 da rabi da muhallansu.

Wannan hare-hare dai na zuwa a dai dai lokacin da ake zabga ruwan sama a wannan yanki,a wani yanayi da ake fama da karancin wuraren fakewar jama’a ta yadda dubunnan kananan yara ke rayuwa a sararin subhana cike fa fargabar yiwuwar kai hari daga Isra'ila a kowanne  lokaci.

Ko a daren jiya Isra'ilan Yahudu ta kai hare-hare sansanonin ‘yan gudun hijira na Al-Aroub da ke arewacin Hebron sai takwaransa na Shuafat da ke gab da birnin Qudus kana Beit Lakia a yammacin Ramallah, wadanda dukkaninsu ta kashe tarin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.