Isa ga babban shafi

An kashe mana sojoji sama da 100 a Gaza - Isra'ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, an kashe mata sama da sojoji 100 tun bayan barkewar yaki tsakanin kasar da mayakan Hamas a Zirin Gaza fiye da watanni biyu da suka gabata.

Wasu daga cikin sojojin Isra'ila da ke yaki a Gaza.
Wasu daga cikin sojojin Isra'ila da ke yaki a Gaza. REUTERS - AMIR COHEN
Talla

 

Ko a jiya Lahadi sai da aka kashe wasu daga sojojin Isra'ila a yayin da suke tsaka da fafatawa a yankin kudancin Zirin Gaza kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.

Alkaluman da sojojin suka fitar sun nuna cewa, akwai dakarun Isra'ila dubu 1 da 593 da suka samu raunuka da suka hada da 559 da suka jikkata a lokacin da suke kokarin kutsawa cikin Gaza ta kasa.

Sanarwar rundunar sojin na zuwa bayan wata jaridar Isra'ila ta Yedioth Ahronoth ta rawaito cewa, sama da sojojin kasar dubu 5 aka raunata a Gaza tun bayan barkewar yakin, yayin da a hukumance, Ma'aikatar Kula da Sojin Kasar ta ce, dubu 2 daga cikinsu sun zama masakai. 

Kazalika alkaluman asibiti sun nuna cewa, adadin sojojin da aka raaunata sun rubanya alkaluman gwamnati sau biyu kamar yadda jaridar Heeretz ta kasar ta ambato.

Isra'ila ta kaddamar da yaki kan Gaza ne a ranar 7 ga watan Oktoba domin mayar da martani kan harin da mayakan Hamas ta fara kai mata, inda ta kashe mata mutane kimanin dubu 1 da 400.

Bayanai na nuni da cewa, sama da Falasdinawa dubu 17 da 997 ne suka rasa rayukansu akasarinsu mata da kananan yara, yayin da dubu 49 da 229 suka jikkata a yakin na Isra'ila da Hamas a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.