Isa ga babban shafi

An wari gari da mummunar arangama a birnin Khan Yunis na Gaza

Bayanai daga Gaza na cewa Isra’ila ta yi wani barin wuta mai muni a kudancin Gaza da safiyar nan, jim kadan bayan barazanar Hamas na cewa babu wani dan Isra’ila da take rike da shi da zai bar yankin da ran sa matukar ba’a cika sharrudan da ta gindaya na sakin mayakan ta da aka kama ba.

Wannan na cikin arangama mafi muni da Hamas ta yi da dakarun Isra'ila  tun bayan barkewar rikicin watanni biyu da suka gabata
Wannan na cikin arangama mafi muni da Hamas ta yi da dakarun Isra'ila tun bayan barkewar rikicin watanni biyu da suka gabata AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Faya-fayan bidiyo da suka fito daga yankin da Safiyar yau, sun nuna yadda tankokin yakin Isra’ila ke ci gaba da nike birnin Khan Yunis yayin da jirage ke ruwan wuta ta sama.

Wannan sabon hari na cikin mafiya muni da aka gani tun bayan barkewar yakin watanni biyu da suka gabata.

Mazauna Yankin na Khan Yunis sun ce tuni tankokin yakin Isra’ila suka mamaye arewa maso kudu na birnin, yayin da jirage ta sama ke barin wuta a yammacin birnin, abinda ya haddasa ruwan wuta a tsakanin bangarorin biyu, kasancewa mayakan Hamas na mayar da martani.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar dinkin duniya ta bukaci dukannin masu ruwa da tsaki su yi gaggawar baiwa kayan agaji damar shiga yankin Gaza, bayan sanarwar ta da ke nuna cewa tuni yunwa ta fara yin ajalin jama’a.

Majalisar dinkin duniyar ta ce a yanzu abubuwan da jama’ar Gaza ke bukata sun zarce kayan abinci, ana bukatar magunguna da kuma jami’an lafiya, la’akari da yadda yakin ya yi ajalin likitocin da ba’a san adadin su ba.

Kawo yanzu dai yakin ya hallaka fararen hula kusan dubu 18, sai wasu dubu 48 da suka jikkata mafi yawa mata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.