Isa ga babban shafi

Rayukan jami'an MDD kusan 100 sun salwanta a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan jiya sun kashe jami’anta 88, adadi mafi yawa na jami’anta da su ka taba mutuwa a yaki guda.

ISRAEL-PALESTINIANS/
ISRAEL-PALESTINIANS/ REUTERS - Ashraf Amrah
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar tare da wasu hukumomin bada agaji da ba na Majalisar ba, sun tabbatar da rasha rasa jami’ansu da dama a wannan rikicin.

Jami'n kiwon lafiya da suka mutu a rikicin Gaza

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministan harkokin kiwon lafiyar Gaza Mai al-Kaila ya ce, a cikin kwanaki 31 da aka yi ana gwabza rikici a yankin Gaza, ma’aikatan lafiya 175 suka rasa rayukansu tare da wasu masu aikin sa-kai 34.

Wasu daga cikin motocin daukar marasa lafiyar Gaza da Isra'ila ta kaiwa hari.
Wasu daga cikin motocin daukar marasa lafiyar Gaza da Isra'ila ta kaiwa hari. REUTERS - STRINGER

Ya ce a cikin wannan lokacin, asibitoci 16 daga cikin 36 da kuma dakunan sha ka tafi 51 daga 72 da ake da su a Gaza suka daina aiki, sakamkon hare-haren Isra’ila ko kuma karewar kayan aiki da man fetur.

Hare-haren cikin daren Litinin

A ci gaba da ruwan bama-baman da Isra’ila ke yiwa yankin na Gaza kuwa, a dare litinin din nan mutane 27 ne suka rasa rayukansu, 15 daga ciki a yankin Tal al-Sultan da 10 a Al-Zawaida sai kuma 2 a Jabalia.

Wasu daga cikin wadanda harin Isra'ila ya shafa da aka kai asibitin Al-Shifa, da ke Gaza.
Wasu daga cikin wadanda harin Isra'ila ya shafa da aka kai asibitin Al-Shifa, da ke Gaza. AFP - BASHAR TALEB

Kawo yanzu ba a samu damar jin yadda lamarin ya ke a wasu yankuna na Gaza ba, sai dai ana ganin ruwan bama-baman da Isra’ila ta yi a cikin daren adadin na iya zarce hakan.

Adadin sojojin Isra'ila da suka mutu a cikin Gaza

Tun bayan fara kai hare-hare ta kasa da sojojin Isra'ila suka yi a cikin yankin Gaza, sojojin kasar 30 ne suka mutu bayan kashe Shahar Cohen Mivtach da ke aiki a karkashin bataliya ta 9.

Wasu daga cikin tankokin yakin da Isra'ila ta girke a Arewacin Gaza.
Wasu daga cikin tankokin yakin da Isra'ila ta girke a Arewacin Gaza. AFP - -

Adadin wadanda suka mutu a Gaza

Hukumomin yankin Gaza sun tabbatar da mutuwar Falasdinawa dubu 9 da dari 8, tun bayan faro rikicin Hamas da Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.