Isa ga babban shafi

Hare-haren Isra'ila kan fararen hula a Gaza na iya zama laifukan yaki - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa a game da yadda hare-haren da Isra’aila ke kai wa tare da kashe fararen hula a yankin Gaza na Falasdinu. 

Sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinawa na Bureij da ke tsakiyar Gaza, wanda Isra'ila ta kaiwa hari a ranar 2 ga watan Nuwamban 2023.
Sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinawa na Bureij da ke tsakiyar Gaza, wanda Isra'ila ta kaiwa hari a ranar 2 ga watan Nuwamban 2023. REUTERS - STRINGER
Talla

Hukumomin da ke aiki karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, sun tabbatar da cewa hare-haeren sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da suka hada da mata da yara kanana. 

Akalla kananan yara 3,500 ne suka rasa rayukansu a Zirin Gaza daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da farmakin daukar fansa, yayin da Hamas ke ci gaba da yin garkuwa wasu yara kanana da dama ‘yan Isra’ila.  

Kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da abin da ya kira cin zarafin bil’adama a wannan yaki, yayin da Antonio Guterres ta bakin mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ke bayyana kaduwarsa a game da hare-haren da Isra’ila ta kai wa sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya. 

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. AP - Niranjan Shrestha

Guterres dai ya bukaci dukkanin bangarorin da ke da hannu a wannan yaki da su mutunta dokokin kasa da kasa da suka jibanci kare hakkin dan adam, inda a nashi bangare shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar ya yi kashedi a game da yiyuwar aikata laifukan yaki a wannan rikici na Isra’ila da Hamas. 

Kokarin fidda baki da ke makale a yankin Gaza

Masar za ta taimaka wajen kwashe baki 'yan kasashen waje kusan 7,000 daga zirin Gaza da yaki ya daidaita, inda jami'ai suka ce ana sa ran mutane 400 za su tsallaka iyakar ta a yau Alhamis. 

Mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Ismail Khairat ta ce Masar na shirin karbar bakin da kwashe 'yan kasashen waje daga Gaza ta mashigar Rafah. 

Khairat ta ce hakan ya shafi mutane kusan dubu 7 daga kasashe sama da 60, amma sanarwar ba ta bayar ba ta  yi bayani ko kayyade lokaci da za a kammala aikin ba. 

A bangaren Falasdinawa, Hisham Adwan, daraktan iyakar Rafah a Gaza, ya ce ana sa ran mutane kusan 100 da suka jikkata da kuma baki 400 da ke dauke da shedar zama 'yan fiye da daya ciki har da 'yan kasar Amurka za su tsallaka a yau Alhamis. 

Falasdinawa da ke da kafin shedar zaman wasu kashashe, na jirar a tantancesu don barin yankin Gaza.
Falasdinawa da ke da kafin shedar zaman wasu kashashe, na jirar a tantancesu don barin yankin Gaza. © IBRAHEEM ABU MUSTAFA / Reuters

Hukumomin Masar sun ce baki ‘yan kasashen waje 361 da masu shaidar zaman ‘yan kasashe biyu ne suka shiga Masar a ranar Larabar, kari akan adadin da a baya aka ce 335 da aka baiwa damar fita. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.