Isa ga babban shafi

Halin da ake ciki game da rikicin Hamas da Isra'ila

Yau aka cika kwana 26 da  fara gwabza rikicin Hamas da Isra’ila, wanda ya biyo bayan harin da Hamas din ta kai da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu daya da dari 4 a Isra'ila, adadi mafi yawa da kasar ta taba asara sanadiyar hare-hare, sannan kuma suka yi garkuwa da sama da mutane 230.

Yadda mutane ke ci gaba da laluben wadanda burabuzan gine-gine suka danne.
Yadda mutane ke ci gaba da laluben wadanda burabuzan gine-gine suka danne. AP - Abed Khaled
Talla

Tun bayan faruwar hakan, Isra’ila ta fara ruwan bama-bamai a yankin Gaza, wanda ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinu ta ce ya kashe mutane dubu 8 da dari 796, kashi biyu bisa uku na wancan adadi mata ne da yara.

Bari muyi duba kan wasu abubuwa 5 da suka faru a wannan yaki cikin sa’o’I 24 da suka gabata:

Bada damar shigar da wadanda suka samu raunuka Masar daga Gaza

Wannan ne dai karo na farko da Masar ta bude iyakarta ta Rafah don baiwa Falasdinawa da ke son tsere wa hare-haren Isra’ila, ciki kuwa har da wasu ‘yan kasashen waje da kuma masu dauke da kafin shedar zama ‘yan kasa na fiye da guda, damar shiga cikin kasar.

Motocin daukar marasa lafiya na Gaza a lokacin da suke kokarin ketara iyakar Rafah ta Masar, yau 1 ga Nuwamba 2023. (AP Photo/Hatem Ali)
Motocin daukar marasa lafiya na Gaza a lokacin da suke kokarin ketara iyakar Rafah ta Masar, yau 1 ga Nuwamba 2023. (AP Photo/Hatem Ali) AP - Hatem Ali

A cewar alkalumar da hukumar Masar suka fitar a yammacin Laraban nan, Falasdinawa 76 da suka samu munanan raunuka ne suka isa kasar tare da 'yan kasashen waje da ke makale a Gaza su 335, ta iyakar Rafah.

Hamas ta ce 7 daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su sun mutu

A Laraban nan ce kungiyar  Hamas ta tabbatar da mutuwar mutane 7 daga cikin wadanda ta ke tsare da su, ciki harda masu dauke da shedar kasashen waje 3, bayan harin da Isra’ila ta kai Arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliyah.

Wasu daga cikin wuraren da hare-haren Isra'ila ya lalata a sansanin Jabaliyah a Gaza.
Wasu daga cikin wuraren da hare-haren Isra'ila ya lalata a sansanin Jabaliyah a Gaza. © STRINGER / Reuters

Harin na ranar Talata dai ya kashe mutane da dama, sai dai fara ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da wannan yakin, duk da cewa sojojin kasarsa sun tabbatar da mutuwar jami’ansu 11 a cikin Gaza.

Sake katsewar sadarwa a Gaza

An sake samun katsewar sadarwa a yankin Gaza a Laraban nan, wannan ne karo na biyu da ake fuskantar irin wannan matsala a yankin, tun bayan faro yakin Hamas da Isra’ila a ranar 7 ga watan daya gabata.

Hukumar kula da sadarwa da duniya ta tabbatar da hakan, inda ta ce kusan dukkanin yankin zirin Gaza da ke da yawan mutane miliyan 2 da dubu dari 4 abin ya shafa.

Gargadin kasashen Iran da Jodan

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Laraban nan ya bukaci kasashen Musulmi da su dakatar da huldar kasuwanci da Isra'ila, ciki har da ta makamashi, sannan kuma ya caccaki gwamnatocin kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Amurka, kan rashin  goyawa Falasdinawa baya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei. AP

Haka nan ministan tsaron kasar Mohammad Reza Ashtiani, ya gargadi kasashen Turai game da taimakon da su ke baiwa Isra’ila, inda ya ce su guji fushin kasashen Musulmi.

Ita kuwa kasar Jodan da ke da kyakyawar alaka da Isra'ila a yankin kasashen Larabawa,sanar da yiwa jakadanta da ke kasar Isra'ila kiranye ta yi, sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Gaza.

Ziyarar Blinken a yankin Gabas ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai sake kai wata ziyara Isra’ila don gudanar da tattaunawa a ranar Juma'a, sannan ya ziyarci wasu manyan kasashen yankin a kokarin da Washington ke yi na neman hanyoyin dakile rikicin Isra'ila da Hamas, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.