Isa ga babban shafi

Rundunar Sojin Isra'ila ta tabbatar kisan dakarunta 258 a harin Hamas

Rundunar Sojin Isra’ila ta tabbatar da kisa dakarunta 258 a hare-haren da kungiyar Hamas ta kai mata ranar Asabar din da ta gabata, lamarin da ya kai ga barkewar yaki tsakanin bangarorin biyu.

Wasu Sojin Isra'ila a yankin da Hamas ta kaddamar da farmaki.
Wasu Sojin Isra'ila a yankin da Hamas ta kaddamar da farmaki. REUTERS - Ronen Zvulun
Talla

Kakakin rundunar Sojin ta Isra’ila Daniel Hagari a jawabin kai tsaye da ya gabatar game da adadin Sojojin da Isra’ilar ta yi asara, ya ce zuwa yanzu na gano iyalai da ‘yan uwan sojojin kasar 258 da suka mutu.

Kafin yanzu dai Isra’ila ta sanar da mutuwar dakarunta 169 ne gabanin karuwar adadin a yau Juma’a.

Da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata ne, Hamas ta kaddamar da jerin hare-hare ta ruwa da kasa da kuma sararin samaniya kan Isra’ila wanda ke matsayin hari mafi muni da kungiyar ta kaddamar kan kasar ta Yahudawa a gomman shekaru da suka gabata.

Zuwa yanzu fiye ‘yan Isra’ila dubu 1 da 300 suka mutu a hare-haren na Hamas ko da ya ke dakarun Isra’ila sun mayar da martani tare da kashe Falasdinawa fiye da dubu 1 da 300 a yankin Zirin Gaza baya ga tilasta musu ficewa daga yankin gabaki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.