Isa ga babban shafi

Tunisiya ta ki karbar tallafin da EU ta ware mata kan matsalar 'yan cirani

Shugaban kasar Tunisiya, Kais Saied, ya ce kasarsa ta ki karbar kudaden agajin da Tarayyar Turai ke ware mata, wanda adadinsu ya ce sun ci karo da yarjejeniyar da aka kulla a watan Yuli tsakanin bangarorin biyu.

Firaministar Italiya, Georgia Meloni, daga hagu, tare da shugaban Tunisiya Kais Saied daga hagu, a birnin Tunis ranar 6 ga watan Yuni, 2023.
Firaministar Italiya, Georgia Meloni, daga hagu, tare da shugaban Tunisiya Kais Saied daga hagu, a birnin Tunis ranar 6 ga watan Yuni, 2023. via REUTERS - TUNISIAN PRESIDENCY
Talla

A ranar 22 ga watan Satumba ne hukumar Tarayyar Turai ta sanar da cewa, za ta fara ware kudaden da aka tanada a karkashin yarjejeniyar da kasar Tunisia, domin rage yawan bakin haure da ke shiga nahiyar daga kasar.

Hukumar ta bayyana cewa, za a ware Yuro miliyan 42 daga cikin miliyan 105 na aikin taimakon da aka tanada a karkashin wannan yarjejeniya domin yaki da matsalar kwararar bakin haure cikin gaggawa.

"Saboda haka, Tunisiya ta ki amincewa da abin da EU ta sanar a 'yan kwanakin nan", in ji Saied.

Ya bayyana cewa wannan kin amincewa da irin tsarin ba saboda adadin da aka ware wa kasarsa bane, a’a saboda wannan shawarar ta sabawa yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a Tunis.

A cewar Hukumar Tarayyar Turai, za a yi amfani da wannan tallafin ne a wani bangare na gyaran jiragen ruwa da masu tsaron gabar tekun Tunisiya ke amfani da su, da kuma hada kai da kungiyoyin kasa da kasa domin kare lafiyar bakin haure da kuma ayyukan mayar da wadannan 'yan gudun hijira daga Tunisiya zuwa kasashensu na asali.

Yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Tunisiya da EU ta kuma tanadi bayar da tallafin Yuro miliyan 150 a shekara ta 2023, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tattalin arziki.

Kasashen Tunisiya da Libya, sun kasance manyan hanyoyin da dubban bakin haure kan yi amfani da su wajen isa tekun Mediteriniya domin shiga Turai da kuma kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.