Isa ga babban shafi

'Yan cirani dubu 2 da 500 sun mutu a tekun Mediterranean cikin watanni 9- MDD

Hukumar kula da ci rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai ‘yan cirani akalla dubu 186 da suka ratsa tekun Mediterranean don samun mafaka a kasashen Turai da kaso mai yawa a Italiya. 

Wasu 'yan ci rani a kokarin tsallakawa Nahiyar Turai ta Tekun Mediterranean.
Wasu 'yan ci rani a kokarin tsallakawa Nahiyar Turai ta Tekun Mediterranean. AP - Cecilia Fabiano
Talla

Rahoton da hukumar ta UNHCR ta fitar a yau Juma’a ta ce daga watan Janairun shekarar nan zuwa ranar 24 ga watan Satumban da mu ke ciki, adadin ‘yan ciranin da yawansu ya kai dubu biyu da 500 ne ko dai suka mutu ko kuma suka bace a tsakar tekun na Mediterranean a kokarin tsallakawa Turai.

Wannan rahoto na UNHCR na zuwa a dai dai lokacin da shugabannin kasashen EU 9 ke gudanar da wani taro yau Juma’a a Malta karkashin jagorancin Ursula von der Leyen da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar ta ‘yan ci rani, kwana guda bayan ministan harkokin wajen kungiyar ya gabatar da wata doka da ke da nufin dakile kwararar masu neman mafaka a sassan Turai

Shugaban hukumar ta UNHCR Ruven Menikdiwela yayin jawabinsa gaban zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce alkaluman ‘yan ciranin da suka mutu a bana ya kusan rubanya adadin da aka gani a bara lokacin da ‘yan ciranin dubu 1 da 680 suka mutu a kokarin tsallakawa Turai ta tekun, ciki kuwa har da wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga gano gawarwakinsu ba.

Alkaluman hukumar ya yi kiyasin cewa ‘yan cirani dubu 102 daga Tunisia sun ratsa tekun wanda ke nuna karin kashi 260 idan an kwatanta da wadanda suka ratsa a bara, yayinda adadin mutum dubu 54 suka ratsa tekun zuwa Turai daga Libya.

Rahoton na UNHCR ya bayyana cewa an yi nasarar tseratar da akalla mutane dubu 31 yayinda aka dakile kwararar wasu dubu 10 da 600 wadanda suka nufaci ratsa Turai ta Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.