Sojojin ruwan Italiya sun ceto bakin haure 539 a tekun mediterranean
Sojojin ruwan da ke tsaron gaɓar tekun Italiya ya kuɓutar da bakin haure 539 daga wani jirgin kwale-kwalen kamun kifi da ya nutse daga tsibirin Lampedusa.
Wallafawa ranar:
Mata da yara na daga cikin wadanda ke cikin jirgin, da ya taso daga gabar ruwan kasar Libya, kuma rahotani sun ce akwai alamun cin zarafi a garesu.
Wata likita daga kungiyar agaji ta likitoci MSF, Alida Serrachieri, ta ce da yawa daga cikin bakin hauren sun gamu da munanan raunuka a Libya yayin da suke jiran jirgin ruwa da zai kai su Turai.
Masu bincike na duba yiwuwar watakila 'yan ciranin an daure su a gidan yari a Libya, in ji kafofin yada labarai na cikin gida. Amma masu gabatar da kara a Italiya sun bude bincike kan abin da ya faru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu